Yadda labaran wasanni kwallon kafa ya kasance ayau laraba
Wasan hamayya 'EL CLASICO' za'a buga da karfe daya na rana a ranar 26 October 2019 a filin wasa na Camp nou.

Gidan telebijin Wanda yake watsa labarai na gasar laliga dake kasar Spain wato (Movistat)shi ya sanar da hakan yanda za'a buga wasan.

A shekara biyu da suka gabata shekarar 2017 December a filin wasan real Madrid wato Santiago bernabeu an buga wasanne da karfe daya na rana amma wannan shine karo na farko da za'a buga wasan a camp nou a irin wannan lokaci.


MESSI YA SAMU RAUNI A WASANSU DA VILLA REAL RANAR TALATA.

Tun farkon fara gasar laliga messi baisamu damar buga wasa hudu ba sakamakon rauni daya samu kafin a fara gasar.

Ya buga wasansa na farko da suka fafata a wasan nahiyar zakarun turai sai dai kuma ya fara wasanne a benci inda  yakara zama a benci a wasansu da sukayi rashin nasara a hannun Granada daci biyu babo ko daya.

Dan wasan bayan Anje hutun Rabin lokaci sai aka canja shi da Ousman demble bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Bayan antashi daga wasanne kociyan kungiyar tasa Valverde ya tabbatar da dan wasan yasamu rauni (groin) a kafarshi.

KOCIYAN LIVERPOOL JURGEN KLOOP YANASON TSOHON CAPTAIN DIN KUNGIYAR GERRARD YAZAN KOCIYAN KUNGIYAR.

Tsohon captain din kungiyar ta Liverpool wato Steven Gerrard shine Wanda yake da basirar maye gurbin jurgen kloop inji kociyan kungiyar ta Liverpool.

Ya bayyana cewa idan kungiyar ta sallameshi wataran ya taba zaban kenny dalglish a matsayin Wanda zai maye gurbinshi amma kuma a lokacin sai yace zaiyi wahala asaka Gerrard a matsayin nabiyu.

Yacigaba da cewa yanzu idan aka tambayeshi waye yake binshi da soyayya a harkar koyarwarshi to zaice Gerrard kuma yace zai taimakeshi a lokacin da yake bukatar.

Kuma yace shi ba mutum bane mai kishi bakinciki a harkar kuma tuni na bayyyana masa kaina idan yana bukatar taimako zai taimaka masa.

JERIN YAN WASA GOMA A MATSAYIN GWARAZAN YAN WASAN DUNIYA.

Lionel messi yalashe kyautar Dan kwallo na duniya (BEST FIFA PLAYER OF THE YEAR)

1.Lionel messi (Barcelona/Argentina) maki 46.

2.Virgil van dijik(Liverpool/Netherlands) maki 38 yakedashi.

3.Cristiano Ronaldo (Juventus/Portugal) maki  36 yakedashi.

4.Mohammad salah (Liverpool/Egypt) maki 26

5.Sadio mane (Liverpool/Senegal)maki 26.

6.Kylin mbappe (PSG/France) maki 17.

7.Frenkie de jong (Ajax/Barcelona/Netherl.)
Maki 16.

8.Eden hazard (Chelsea/R.Madrid/Belgium) maki 16.

9.De light (Ajax/Juventus/Netherlands) maki 9

10.Harry Kane (Tottenham/England) maki 5.