Abubuwan da suke lalata batirin waya da yadda zaka kiyaye

Assalam barkanku da wannan lokaci kamar yanda muka saba a kullum muna kawo muku labarai bangare daban daban to a yauma kamar kullum ne.

Abinda muka zo muku dashi a yau shine bayanai akan abubuwan da suke lalata batirin wayar musamman wayar zamani wato android.

Haka kuma zamuyi bayani akan yadda zaku kiyaye wannan batirin na wayar taku domin gudun matsala karta sameshi.

Wasu dayawa zakaga sunfitar da kudi dayawa sun sayi waya amma kuma saikuga dafarko tana rike chaji amma kuma daga karshe saikuga ta daina rike chaji kwata-kwata bata dadewa.

Zakuyi tunanin daga matsalar wayar ne haka suka yita kokuma sukayi batirin amma sam bahaka bane daga matsalarku ce yanayin yanda kuke mata.

Duk da munriga munsan cewa akwai wayar da take da rike chaji sosai akwai wacce bata rike chaji amma kuma dukda haka zakuga wata rashin rike chajin yayi yauwa.

ABUBUWAN DA SUKE LALATA BATIRIN WAYA.

1.Na farko shine cinye chajin batirin yayi karkaf ma'ana tayi shutdown da kanta ta dauke to wannan yana iya haifar ma batirin da Marsala.

2.Nabiyu kuma yawan chanje chanjen chaja ita waya bata cika son ana yawan chanja mata chaja ba ana bukatar kayi amfani da chaja daya.

3.Aje waya yayin da take chaji akan katifa akwai bukatar ka ajiye wayarka akan teburi ko a wani waje da kasan ba katifa ba.

4.Abu nahudu shine aje waya a wuri me sanyi
kokuma wuri me danshi inda yakeda lema sosai misali yanzu ka ajiye wayarka a wuri me sanyi zuwa wani lokaci ka duba zakaga batirin yayi kasa to wannan shima yana lalata batirin.

YADDA ZAKA KIYAYE BATIRINKA.

Idan kaga wayarka tayi low battery ma'ana chajinka yayi kasa saika ajiyeta haka karka bari tayi shutdown suka.

Kakiyaye inda zaka aji wayarka yayin da take chaji da lokacin da bata chaji idan ka kiyaye karka barta a wuri me lema dakuma wuri me sanyi.

Kasamu chaja guda daya me kyau me karfi wacce takema chaji sosai normal bata baka matsala to ka rike ta karkayi wasa da ita.

Karka yarda ka ajiyeta a kayifa  a yayin da take chaji idan tagama chaji ka cireta to zaka iya ajiyewa.

Matukar kukabi wadannan dokoki to zaiyi wahala kaga batirinka yana yawan samun matsla a koda yaushe.

Anan muka kawo karshen bayaninmu na yau saikuma lokaci nagaba,  kuci gaba da kasance wa damu a shafin mu na yanar gizo zazzaumedia.com.ng muna godiya.