Duk duniya babu kamar Ronaldo a kwallon kafa inji figo.


DUK DUNIYA BABU KAMAR C.RONALDO INJI FIGO.

Tsohon da wasan real madrid da kuma kungiyar kwallon kafa ta inter milan , Luise figo ya bayyana cewa yanzu babu kamar c.ronaldo a duniya indai ana maganar kwallon kafa ne.

Figo ya bayyana wannan maganar ne bayan da danwasa c.ronaldo ya kafa wani babban tarihi, wanda manyan yan wasan da suka gabata basu samu damar kafa tarihi kamarshi ba.

C.Ronaldo yaci kwallo ta dari bakwai (700) a rayuwarsa ta kwallon kafa ranar litinin a wajen neman gurbin shiga kofin nahiyar turai a karawar da Portugal tayi da Ukraine, kuma dan wasan ne yayi nasarar jefa kwallo daya a bugun dagakai sai mai tsaron gida inda Ukraine tayi nasara daci biyu da daya (2-1).

Yayi nasarar jefa kwallo ta 700 a cikin wasanni 973 daya buga a duniya, hakan yana nufin yakan jefa kwallo sau daya a fafatawa 458 kuma kwallon dayaci Ukraine tazama ta 95 da yacima tawagarsa ta Portugal inda yake biye da Ali Daei dan asalin kasar Iran da yacima kasarsa kwallo 109 dai dai.

C.Ronaldo ya shiga sahun jerin manyan fitattun yan wasa na duniya da sukaci kwallo 700 ko fiye da hakan, inda ya banbanta da sauran manyan yan wasa wadanda suka hada da messi da sauransu.

C.Ronaldo tsohon dan wasan sporting Lisbon da Manchester united dakuma real Madrid inda yanzu yake buga kwallo a kungiyar Juventus dake kasar italiya.

Dan wasan ya lashe kofuna daban daban manya da kanana wadanda suka hada da kofin nahiyar turai dayaciwa kasarsa ta portugal a wannan shekarar.

Mai bin Ronaldo a baya shine abokin hamayyarsa Lionel messi na Barcelona. Messi yanada kwallaye 672 a duniya kuma bai nuna alamun sanyi ba.

Manyan yan wasa irinsu Pele , Bicam , Romario da Muller ne kadai suka yabacin kwallaye fiye da dari bakwai (700), kuma wadannan yan wasa sunyi shekaru da daina buga wasa.

C.Ronaldo yaci kwallaye 450 kafin barinsa babbar kungiyar kwallon kafa fa Real Madrid .

Kafinnan kuma yaci kwallaye samada guda dari a ingila kungiyar Manchester United.

Kafinnan kuma yaci kwallo biyar a asalin kungiyarsa ta gida wato sporting Lisbon dake Portugal.

Inda kuma yaciwa kasarsa kwallaye 95.

Anan muka kawo karshen labaran sai kuma kuci gaba da kasancewa damu a kullum muna godiya.