Yadda zaka siya 1gb naira dari a mtnAssalam barkanku da wannan lokaci barkanku da kasancewa da shafin mu na zazzaumedia.com.ng.

Duba da yanayinda mukayi na tsadar data Allah ya kawomu lokacin da data yazama wani abu mai mahimmanci acikin rayuwarmu saidai kuma wani abu daya shine datar tayi tsada.

Idan kuka duba kuka gani zakuga tsadar datar yayi yawa amma kuma a yau munkawo muku yanda zaku siya datar cikin sauki da araja batare da kunsha wahala ba.

Ita wannan datar a Latin MTN kawai ake siyarwa damace da sukaba abokan kasuwancinsu ma'ana costumers dinsu wadanda suke amfani da layin kamfanin nasu.

Mun dade mun jima muna neman hanyatda za'abi a samu sauki wajen amfani da yanar gizo ba tare da kasamu matsala ba ko wani Abu makamancin hakan.

Wannan datar ba taturawa bace a'a ita kaitsaye zaka siya da katin cikin wayarka ma'ana balance din da yake wayarka.

Yadda zakayi shine Ku danna *131*100# ka kira ammafa kafin kayi ka tabbatar kanada katin da yakai naira 100 Dari acikin wayar taka.

Idan aka sami sabanin hakan to tabbas bazaiyiba koda ace kobo dayane babu, an bukaci aga wannan naira darinne kawai acikin asusun maka.

Amma idan kanada kudin daya haura naira darin ma'ana yafi dari to sudai naira darin kawai zasu dauka su barmaka sauran kudin ka aciki.

Kuma ita wannan data tanakai kimanin wata daya kafin tayi expire ta palace ta daina aiki gaba daya.

Sannan idan kasiya zakaga wurin auto renew kacireshi kakula dakyau saboda da datarka ta kare zasu cire kudin su baka wata.

Amma idan kacire shikenan bakada matsala zaka kara siya aduk lokacin da kaga damar siya.

Anan muka kawo karshe sai kuci gaba da kasancewa da shafin mu na zazzaumedia.com.ng a kowacce rana mungode.