Hanyoyin da zakabi domin kare Facebook account dinka


Assalam barkanku da wannan lokaci, duba da yanayin da muke ciki yanzu Facebook yazama wani babban bangare kokuma jigo da ake amfani dashi wajen sadarwa.

To amma kuma akwai wani abu kuma nace wasu abubuwa da ya kamata muyi domin Kare wannan account din saboda zaka kirkire shi sannan kayi abokai dayawa da Wanda kasani da wanda baka saniba.

Wani zai kirkire account dinshi na Facebook shekara da shekaru amma rana tsaka saikaji ya rasa wannan account din nashi kuma zaiji haushi matuka.

Shiyasa mukaga ya dace muzauna muyi nazari da tunani domin kawo sauyi a al'amuran to mungode Allah munsamu zamuyi muku bayani yadda zaku fahimta daya bayan daya.

Akwai wasu mutane daban wadanda burinsu shine su shiga cikin asusun naka domin suyi barna wasu kuma wata manufa da daban haka zalika wasu yan damfara ne.

Shiyasa mukaga yadace mufito muyi mutane bayani akan yadda abun yake domin magance matsaloli irin wannan wasu kuma sakaci ne kawai.


ABUBUWAN DAYA KAMATA KAYI DOMIN KARE FACEBOOK ACCOUNT DINKA.

1. Na farko shine ka tabbatar kacire lambar wayarka a (profile) dinka domin wasu na amfani da wannan hanyar su canza lambar wayarsu ta koma ta wani kasan daban suyi dubarar da zasuyi su amsa bayanan sirrinka.

2. Nabiyu kuma kayi amfani da kalaman sirrinka ma'ana (password) domin ka Kate kanka wasu sai su saka sunansu ko lambar wayarsu a wurin kunga wani yana gwadawa shikenan abi a hankali.

3. Abu na uku Kuma shine wasu suna sakaci saisu siyar da wayarsu da Facebook account dinsu akai musamman masu amfani da browser kuma sunyi saving din password dinsu akai tabbas suna ganganci .

Kafin kasiyar da wayarka ka tabbatar kacire account dinka akai saboda wani kar yasamu damar shiga account din naka .

Anan zamu dakata sauran abinda baka ganeba ko baka fahimta ba muna jiran tambayar ka a comments box zaka iyayin magana.

Ku kasance da shafin zazzaumedia.com.ng a kowace rana.