Tsohon da wasan Juventus marchisio ya ajiye takalminsaTsohon dan wasan Juventus  wanda kuka Sani da marchisio ya hakura haka sakamakon shekarunsa sun karu ya fara tsufa.

Dan wasan ya buga wa kungiyar tasa ta Juventus wasa 400, bayan haka kuma ya tashi daga Juventus din ya koma kungiyar zenith St peterburg a shekarar 2018 , a wannan kungiyar ya hadu da rauni kala kala Wanda suka hanashi yin kokari sosai.

Marchisio ya buga ma kasarsa ta italiya wasanni 55, kuma yana daya daga cikin wadanda suka buga wasan karshe nacin kofin nahiyar kasashen turai na 2012 .

Ya fadi cewa yarone shi da ya taso a turai sannan tun asali bashida burin daya wuce ya buga ma kungiyar Juventus kwallo kuma burinnasa ya cika ya buga.

Marchisio ya fara buga wasansa nafarko a shekarar 2006 , daganan kuma yayi karar wasa daya a kaishi zaman aro kungiyar Empoli domin ya samu gogewa.

Dan wasan yayi fama da matsanancin ciwon gwiwa a shekarar 2016, daganan yayita kokarin samun gurbi a Juventus har zuwa lokacin da ya koma zenith din.

Marchisio ya samu nasarori da dama a fannin kwallon kafa nasarorin sunhada da kofin da ake kira Italian cup har sau hudu sannan aje wasan karshe nacin kofin zakarun turai.

KUNGIYAR KWALLON KAFA TA JUVENTUS TA SHIGAR DA SABUWAR KARA DOMIN A BATA KOFINTA NA SERIE A DATA LASHE A SHEKARAR 2005/2006 DA AKABA INTER MILAN.

Juventus za ta karbe Serie A na Inter na 2006


Kungiyar Juventus ta shigar da sabuwar kara kan cewar sai an ba ta kofin Serie A na 2005/06 da Inter Milan ta lashe.

Juventus ce ta yi ta daya a kakar 2006, amma aka bai wa Inter kofin, saboda samunta da aka yi cikin rikicin cefanar da wasa, inda aka hukunta kungiyoyi biyar da suke buga Serie A.

Wannan karon Juventus ta shigar da kara gaban wata kotun sauraren kararrakin wasanni da ke Italiya, bayan da a baya ta sha yin hakan amma ba ta yi galaba ba.


AC Milan ce ta yi ta biyu a 2005/06, amma saboda an sameta da hannu cikin badakalar aka bai wa Inter Milan kofin a kakar.

A kuma kakar Juventus ta kammala Serie A da maki 91, AC Milan ta hada maki 88, ita kuwa Inter Milan ta uku keda maki 76.

A lokacin aka hukunta Juventus da AC Milan da Fiorentina da Lazio da Reggina daidai da laifin da suka aikata.

Hukuncin ya shafi Juventus daga mataki na daya ta koma ta karshe a kasan teburi ta koma buga gasar Serie B, ita kuwa AC Milan aka karbi maki 30 a wajenta.

Hakan ne ya sa Milan ta koma ta uku a teburi aka bai wa Inter kofin Serie A na kakar 2005/06 lokacin da Roberto Mancini.


Juventus wadda take ta biyu a kan teburin bana za ta karbi bakuncin Inter Milan a gasar Serie A ranar Lahadi.

Anan muka kawo karshen labaran namu kuci gaba da kasancewa damu a kullum.