Waye zai lashe kyautar fifa na matasa yan kasa da shekara 21 ?

JERIN YAN WASA 20 MATASA YAN KASA DA SHEKARA 21 WADANDA ZA'A ZABI GWARZO NA 2019.

An bayyana sunayen yan wasa guda ashirin 20 da za'a zabi gwani da za'a baiwa kyautar zinare na 2019 ciki harda dan wasan atletico madrid joao Felix.

Dan wasan gaban joao Felix wanda tauraruwar sa take haskawa sosai tun a tsohuwar kungiyarsa ta benfica kafin yadawo atletico madrid da taka leda.

Ita wannan kyauta an ware tane musamman ga zaratan matasan yan wasan wadanda suke kasa da shekara 21.

Kuma yan jarudu da murubuta labarin wasanni na nahiyar turai ne suka kada wannan kuri'a.

Akwai matthijis de Light tsohon dan wasan Ajax da yanzu yake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus, kuma ya samu
lambar yabo ta karshen shekara kuma yana cikin jerin yan wasan guda 20 da za'a zaba.

Akwai tsohon dan wasan Santos na kasar Brazil wato rodrygo goes wanda yanzu yake babbar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wanda tauraruwar sa take haskawa sosai.

Ingila tanada wakilai da za'a zaba wadanda suka hada da Sancho, Mount, dakuma Phil Foden da sauransu.

Akwai kuma zaratan matasan yan wasan Brazil guda biyu wadanda suka hada da viniciurs Jr da rodrygo goes wadanda suke zaune a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Tabbas yan wasa ne da ake ganin zasu taka muhimmiyar rawa a gasar laliga dake kasar Spain ganin yanayin yanda yan wasan ke taka ledar su.

GA JERIN YAN WASAN GUDA ASHIRIN DIN.

1.Joao Felix (Atletico Madrid).

2.Alphoso davies (Bayern Munich).

3.Viniciurs jr (Real Madrid).

4.Gianluigi donnarumma (AC Milan).

6.Phil Foden (Manchester City).

7.Matteo Guendouzi (Arsenal).

8.Erling Haland (Red Bull Salzburg).

9.Rodrygo goes (Real Madrid).

10.Ansu fati (Barcelona).

11.Nicolo Zaniolo (AS Roma).

12.Ferran Torres (Valencia).

13.Jadon Sancho (Borussia Dortmund).

14.Danyell Malen (PSV Eindhoven).

15.Mason Mount (Chelsea).

16.Kang-in Lee (Valencia).

17.Andriy Lunin (Real Sociedad).

18.Moise Kean (Everton)

19.Dejan Joveljic (Eintracht Frankfurt).

20.Kai Havertz (Bayer Leverkusen).

Sune yan wasan da ake sa ran za'a zabi gwani daya daga cikinsu da za'a baiwa kyautar zinare na 2019.

Dukkanin su kuma yara ne yan kasa da shekara 21 amma kuma yanayin taka ledarsu ta manyan mutane kuma yara ne masu matukar hazaka.

Nan muka kawo karshen labarin kuci gaba da kasancewa da shafin mu a kullum kuma akoda yaushe mungode.