Yan wasan da tauraruwar su ke haskawa a cikin shekaru goma.Anfidda wasu gwarazan yan wasa da tauraruwar su take matukar haskawa daga shekaru goma da suka wuce zuwa yanzu tun daga 2009 zuwa 2019.

Aciki sun hada da Ronaldo da Messi da wasu yan kwallon kafan guda tara 9.

A yayin da shekarar 2020 ke cigaba da matsowa gadan gadan babbar kafar watsa labaran kwallon kafa  ta duniya goal.com ta yanke shawarar fidda wadannan sunaye.

Ta yanke shawarar fitar da sunayen wadanda suke da kwaso kuma tauraruwar su take haskawa a shekara goma da suka wuce kuma har yanzu suna ci gaba da wasan.

Yan kwallo 11 da goal ta ruwaito ta tabbatar da bajintarsu tsawon shekara goma da suka shude mawallafan goal suka zakulo wadannan yan wasa sun hada da Peter Staunton, Stefan Coerts, dakuma Sam Brown.

Sunyi zakuken su ne duba da yanayin kokarin yan wasan a kungiyoyinsu dakuma kasashensu wajen nuna bajintar.

Ga jerin yan wasan da goal ta ruwaito guda 11 da sukafi kokari da hazaka a cikin shekaru goma, gasunan kamar haka.


Mai tsaron gida.1.Manuel Neuer ( Germany/B.Munich).


Yan wasan baya.2.Dani Alves (Brazil/Psg).

3Raphael Varane (France/Real Madrid).

4.Sergio Ramos (Spain/Real Madrid).

5.Marcelo (Brazil/Real Madrid).


Yan wasan tsakiya.


6.Toni Kroos (Germany/Real Madrid).

7.Sergio Busquets (Spain/Real Madrid).

8.David Silva (Spain/Manchester City).


Yan wasan gaba.


9.Lionel Messi (Barcelona/Argentina).

10.Robert Lewandowski (Poland/B.Munich).

11.C.Ronaldo (Portugal/Juventus).

Wadannan yan wasan tabbas sunyi abin azo a gani musamman Cristiano Ronaldo da ya cika kwallaye fiye da dari bakwai a wannan kakar.

Kuma akwai wadanda suka lashe kofin zakarun turai sau uku a jere irinsu.

Varane, Ramos , Marcelo, Kroos dakauma Ronaldo wadanda yan wasan sunyi matukar kokari wajan taka Leda sun taka muhummiyar rawa ta azo a ganin.

Sannan kuma akwai Lionel messi da ya kashe kyau fifa ta bana da sauransu dai .

Anan muka kawo karshen labarin na yau saikuma wani lokacin kuci gaba da kasancewa da zazzaumedia.com.ng.