Labaran kwallon kafa ayau laraba

QUNGIYOYIN DA KADAI SUKA LASHE KOFUNA UKU DA AKE KIRA DA (TREBLE)


Qungiyoyi da suka lashe kofuna uku da ake kira da (Tremble) daga Qarni 21.
Barcelona tasamu irin wannan Nasarar daukar kofunan sau biyu: a shekarar 2009 da 2015.

Bayern Tasamu nasarar daukan wannan kofuna a shekarar 2013

Inter Milan itama tai nasarar kafa wannan Tarihi a shwkarar 2010.

Manchester United ta kafa wannan tarihi a shekarar 1998/99.

PSV Eindhoven itama tana cikin wadannan qungiyoyi a shekarar 1987/88

Ajax itama talashe wadannan kofuna a shekarar 1971-72

Celtic takafa wannan tarihi a shekarar 1966/67

BRAZIL TA DOKE MEXICO A WASAN KARSHE NA KOFIN DUNIYA 'YAN QASA DA SHEKARU 17.

Brazil talashe Kofin Duniya karo na Hudu na yan qasa da Shekaru 17 a hannun qasar Mexico.

Mai Rike da masaukin Bakin Brazil tasamu nasara daci 2-1 Inda dan wasanta Lazaro Vinicius Marques Yasaka mata kwallon data bata nasarar daukan kofin a mintuna 93 a Ranar Lahadi.

Mexico Tadauki kofin a shekarar 2005 da 2011, Inda taso cimma daukar na Uku saidai batakai gaci ba, inda dan wasan Bryan Alonso Gonzalez Olivan yafara cimata kwallo a mintuna na 66th dakai.

Saidai Brazil, ta buga wasan karshen ne agaban tsofin gwarzayen yan kwallon kafar qasar Ronaldo da Cafu.

Brazil ta lashe kofin a Shekarar 1997,1999, 2003 da 2019, inda hakan yasanya saura Dauka daya ta kamo qasar da tafi kowacce yawan wannan kofin Nigeria wadda take da Guda Biyar.

Kociya Selecao Yasamu nasarar cinye wasanninshi Guda Takwas na Gasar.

Qasar Peru wadda ta karbi Bakuncin kofin Duniyar na yan qasa da shekaru 17 a shekarar 2007, itace zata karbi bakunci gasar tagaba da Qasashe 24.

GRIEZMANN YANZU SHINE NA 6 A CIN KWALLAYE A FRANCE

Kwallon da Yaci jiya, Griezmann yanzu yazama dan kwallo na 6 ajerin yan kwallon da sukafi yawan cin kwallaye a qasar France.

Antoine Griezmann izuwa yanzu yabada kwallo guda 7 anci a wasannin share fagen Buga EURO 2020, samada kowanne dan wasa.
JERIN YAN WASA DA SUKAFI CIN KWALLAYE A QASAR FRANCE:

1. Thierry Henry  (51)
2. Michel Platini (41)
3. Olivier Giroud (39)
4. David Trezeguet (34)
5. Zinedine Zidane (31)
6. Antoine Griezmann (30) 🆕
6. Just Fontaine (30)
6. Jean-Pierre Papin (30)

REAL MADRID A KARON FARKO TA SAYARDA BERNABEU A KARAWARSU DA PSG.

Real Madrid tasaida Filin wasa na Estadio Santiago Bernabeu a karon farko a wannan kakar a karawarsu da  Paris Saint Germain a kofin Zakarun Turai.

An fitar da sabon tikiti na shiga kallon karawar tasu, inda za'a saidashi ranar jumu'ah.

Izuwa yanzu Real madrid ta kokarin Ganin yadda zata buto daga Rukuni, bayanda Real madrid din zata karbi bakunci Kylian Mbappe dan wasan da ake ganin~ mawuyacine mai dawo Gidan ba.

PSG tabaiwa magoya bayanta 3,000 damar zuwa kallon karawar domin ganin sun kara mata kwarin gwiwar futowa a Rukuni zuwa zagaye na 16.