Labarin musha dariya masu dadi

Labari na farko : Aljani da mutum uku .

Wasu mutane ne abokai su uku suna cikin tafiya dukkaninsu sun sha wahala sun gaji ga yunwa hakuma kishi sunsha wahala.

Gashi cikin daji ne babu gida gaba babu gida baya harsun fara tunanin mutuwa kawai sabida babu hanyar fita.

Sai suka tsinci wata kwalba a a gabansu harsun fara tunanin ruwa ne aciki suna bude kwalbar saiga wani hayaki a ciki ya fito ya tashi sama.

Hayakin nagama fita daga cikin wannan kwalbar saiya hadu waje daya saiga wani aljani kato a gabansu.

Wannan aljanin ya fitowa sai yayi dariya yace kowanne acikinsu ya fadi abinda yake bukata yayi masa.

Ai nan take sai kowanne acikinsu ya fara murna sakamakon wannan zance da sukaji aljanin ya fada.

Sai daya daga cikinsu na farko yace yanaso a kaishi Dubai abude masa kasuwanci sannan a bashi katuwar kwantena acika masa da kudi.

Sai aljanin yace masa shikenan abinda kake bukata sai yace masa "eh" sai aljanin yace to shikenan.

Ya umarceshi da ya rufe idonsa yana rufe ido sai aljanin yace masa bude yana budewa kawai yaga dukkanin abinda ya bukatar.

Shikuma na biyun aka tambayeshi me yake bukata ayi masa a rayuwarsa ta duniya gaba daya.

Sai yace akaishi America a gina masa gida a bashi motoci abasa kudi wanda bazasu kareba.

Sai aljanin yace shikenan babu wani abinda kake bukata a rayuwaka sai nabiyun yace "eh".

Shikenan yace masa rufe idonka yana rufewa a mintuna kadan kawai sai yace masa yabude yana budewa sai shima yaga duk abinda yace yana bukatar.

Saura na karshen aljani ya tambaya na karshe me yake bukata shikuma yace yanaso a dawo masa da sauran yan'uwansa.

Yace masa rufe idonka yana rufewa sai aljanin yace masa ya bude idonsa yana budewa kawai saiga sauran yan'uwan nasa sun dawo wurinshi.

Kawai aljanin ya zama hayaki yabi iska ya tafi shikenan.

Labari na biyu : Nasan za'ayi sanyi cikin dare.Wani saurayi ne yaje fira wajen budurwarsa, suna cikin fira saiga hadari ya hadu a gari za'ayi ruwan sama.

Ganin yadda garin yake sai surikin nasa yace ma yarinyar tasa tace masa za'a basa daki ya kwana saboda ruwa.

Saika ruwa ya sakko sai saurayin aka bashi daki harya shiga saiyace bari yaje ya dawo saiya fita.

Sai gashi ya dawo a jike jikinsa akace masa ina yaje sai yace ai yaje gida ne ya dauko abin rufa sabida yasan za'ayi sanyi cikin dare.