Maurinho yazama sabon coach din Tottenham


TOTTENHAM TA BAYANNA MOURINHO A MATSAYIN SABON KOCIYANTA.

Qungiyar Tottenham Hotspur Ta sanar da daukan Jose Mourinho a matsayin sabon  kociyan qungiyar, da zai cigaba da Jan ragamar kungiyar inda yasanya kwantaragin shekaru Uku, hakan zaikashi har shekarar 2022/23.

Qungiyar ta sallami Tsohon kociyanta Mauricio Pochdttino ranar Talata Biyo bayan Fara gasar wasan bana da Koma baya, duba da shekarar data gabata yaje wasan karshen na kofin zakarun Turai, kuma bai dauka ba, haka gasar premier league bai kasance saman Teburi ba.

Tottenham tana mataki na 14 a Teburin bayan samun Nasarar Wasanni Uku acikin wasanni 12 data buga a wannan shekarar.

Magana akan baiwa, mourinho yace:- Naji karfi da tagomashi dana samu shiga qungiyar da take da abubuwa masu kyau da magoya baya na musamman. Sannan tanada hazikan yan wasa wanda suka jima suna nuna bajintarsu a qungiyar. Aiki da wadannan yan wasan tabbas zai taikamin akan abinda nakeao." Inji-Mourinho.


NEYMAR ZAI BIYA £17M DAGA ALJIHUNSHI DOMIN KOMAWA BARCELONA.

Neymar Zai biya £17m daga kudinshi domin ganin yiyuwar komowarshi Barcelona a kakar wasa mai zuwa.

Dan wasan qasar Brazil din yaso komowa tsohuwar qungiyar tashi Nou Camp a kasuwar yan wasan data gabata, inda Barcelona ta zauna tautaunawa da Paris Saint Germain saidai hakan bata yiwuba.

Neymar yaki amincewa da Tayin PSG na Sabunta kwantaraginsa har zuwa 2025. bayanda shugaban qungiyar PSG Nasser Al-Khelaifi yaki barinshi yakoma Barcelona a farkon kakar wasa. tautaunawa tsakanin Mahaifin Neymar da Psg akan Barinshi zuwa Barcelona bata samu karbuwa agun mahukunta na Psg.

Rahoto ya tabbatar dacewa da alamun,  dawowar Neymar Spain, Neymar ya amince zai biya £17m a cikin £153m wanda hakan zai bashi damar tafiya acikin kwantaraginsa.

Haka zalika a wani Rahoto da jaridar ta fitar ta bayyana tsohon dan wasan Santos din zai iya tafiya a wannan adadin kudin bayan ya cika shekaru uku a kwanataraginsa na shekaru biyar da Psg.

Wata yarjejeniya kuma tana nuna Ivan Rakitic da dan wasan baya Jean-Clair Todibo Barcelona zatai amfani dasu domin share hanyar zuwan Neymar.

Anan muka kawo karshen labaran kuci haba da kasancewa da mu a kullum.